JAMI'AR KOYON HARSUNAN

WAJE TA BEIJING

TAKAITACCEN BAYANI

发布时间:2019-05-15

TSARIN KARATU DA FATARAR KARATU

AKWAI FATARAR KARATU GUDA 2 A KO WACE SHEKARA WATO NA LOKACIN BAZARA DA LOKACIN KAKA. AN FARA SABON FATARAR KARATU DAGA LOKACIN KAKA, WATO DAGA FARKON WATAN SATUMBA NA BANA ZUWA TSAKIYAR WATAN JANAIRU NA SHEKARA MAI ZUWA. YAYIN DA FATARAR KARATU NA BAZARA YA FARA DAGA KARSHEN WATAN FEBRAIRU ZUWA TSAKIYAR WATAN YUNI. A KO WACE SHEKARA AKWAI LOKACIN HUTU NA ZAFI DA NA SANYI, LOKACIN HUTU NA ZAFI, A KAN SAMU HUTU NA TSAWON WATANNI BIYU WATO YULI DA AUGUSTA. YAYIN DA LOKACIN HUTU NA SANYI, A KAN SAMU HUTU NA MAKWANNI 4, WATO AN HADA LOKACIN HUTU DA BIKIN BAZARA TARE. A LOKACIN HUTU, JAMI’AR TA KAN SHIRYA KWAS NA KOYAR DA SINANCI CIKIN GAJEREN LOKACI.

KARATU DON SAMUN DIGIRI

1.TSARIN KARATU DON SAMUN DIGIRI NA FARKO YA KAN SHAFE SHEKARU 4, BAYAN DA AKA KAMMALA KOYAR DA DUK ABUBUWA BISA SHIRIN DA AKA TSARA, KUMA AN CIMMA NASARA KAN AMSA TAMBAYOYIN MALAMAI GAME DA KUNDIN DA AKA RUBUTA, ZA A SAMU TAKARDAN SHAIDA KARATU, WADANDA SUKA CANCANCI DON SAMUN DIGIRI, ZA A DANKA MUSU TAKARDAR DIGIRI NA FARKO.

2.TSARIN KARATU DON SAMUN DIGIRGIRI YA KAN SHAFE SHEKARU 2 KO 3, YA DANGANTA DA MABAMBANTA FANNONIN KARATU. DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE ZA SU YI KARATU TARE DA SINAWA, BAYAN DA SUKA KAMMALA KARATU DA KUNDI, KUMA SUKA CIMMA NASARA KAN AMSA TAMBAYOYIN DA AKA YI MUSU,ZA A SAMU TAKARDAR SHAIDA KARATU DA DIGIRGIR.

3.TSARIN KARATU DON SAMUN DIGIRI NA UKU, YA KAN SHAFE SHEKARU 3, BAYAN DA AKA KAMMALA KARATU DA CIMMA NASARAR NAZARIN WASU ABUBUWA, DA KAMMALA RUBUTA KUNDI, ZA A YI MUSU AMSA TAMBAYOYI GAME DA KUNDIN, BAYAN DA AKA KAWO KARSHEN WADANNAN AYYUKA,ZA A SAMU TAKARDAR SHAIDA KARATU DA DIGIRI NA UKU.

KARATU BA DON SAMUN DIGIRI BA

  1. DALIBAN HORASWA: TSARIN KARATU YA KAN SHAFE RABIN SHEKARA KO SHEKARA GUDA, KUMA YA DANGANTA DA ROKON DA AKA BAYAR DON TSAWAITA LOKACIN KARATU. BISA TSARIN DA AKA BAYAR, ZA A HORAR DA SINANCI KO SAURAN FANNONIN KARATU, BAYAN DA AKA KAMMALA KARATU DA CIMMA NASARAR JARRABAWA, ZA A SAMU TAKARDAR SHAIDAR HORASWA.

  2. DALIBAN HORASWA CIKIN GAJEREN LOKACI: YANZU, AN KAFA KWAS DIN HORAR DA HARSHEN SINANCI CIKIN GAJEREN LOKACI. ZA A YI AMFANI DA KWAS DON YAWON SHAKATAWA DA KARATU A KASAR SIN DA KARA SANIN AL’UMMAR SINAWA. A LOKACIN ZAFI,AKWAI KWAS DIN NA MAKWANNI 8 DA NA MAKWANNI 4 KANA DA NA MAKWANNI .

  3. 3. A LOKACIN SANYI, A KAN SHIRYA KWAS DIN NA MAKWANNI 4. A KAN KOYAR DA SINANCI DAGA SAFIYAR LITININ ZUWA JUMMA’A NA KO WANE MAKO, YAYIN DA A KAN KOYAR DA AL’ADUN SINAWA DA YAMMA, KUMA A KO WANE MAKO, A KAN SHIRYA YAWON BUDE IDO A BIRNIN BEIJING. BAYAN DA DALIBAI SUKA SHIGA CIKIN JAMI’AR, ZA SU SAMU TAKARDAR DALIBAI‘YAN KASASHEN WAJE NA BFSU, KUMA BAYAN DASUKA KAMMALA KARATU, ZA A SAMU TAKARDAR SHAIDA KARATU NA JAMI’AR.

NEMAN SHIGA JAMI’AR DA SHIRYE-SHIRYEN DAUKAR DALIBAI

  1. NEMAN SHIGA JAMI’AR: (DAGA TSAKIYAR WATAN AFRILU ZUWA FARKON WATAN YUNI DON NEMAN KARATU A LOKACIN KAKA; DAGA TSAKIYAR WATAN OKTOBA ZUWA FARKON WATAN JANAIRU DON NEMAN KARATU A LOKACIN BAZARA)DALIBAI ZA SU IYA DUBA SHAFIN YANAR GIZO(HTTP://STUDY.BFSU.EDU.CN) DON YIN RAJISTAR NEMAN SHIGA CIKIN JAMI’AR, A SA’IDAYA KUMA, YA KAMATA A TURA FASFO DA TAKARDUN SHAIDU IRI NA GURZAWA ZUWA SHAFIN. A LOKACIN, ZA A BINCIKA TAKARDUN DA AKA TURA, KUMA IDAN ANA BUKATAR KARIN TAKARDU, ZA A SANAR DA KU CIKIN LOKACI. KAZALIKA, ZA A SHIRYA JARRABAWA, ZA A DUBU TSARIN RAJISTA, DON SANIN MATAKAN DA AKE CIKI.

  2. DAUKAR DALIBAI: BAYAN DA JAMI’AR TA DAUKE KU, ZA A SANAR DA KU, GAMI DA BAYAR DA TAKARDUN DAUKAR DALIBAI, DA TAKARDAR IZNIN SHIGA KASA TA VISA NA ZUWA KARATU A KASAR SIN (JW202),DA SAURAN TAKARDU. ANA BUKATAR MAKWANNI A KALLA 4 ZUWA 5 BAYAN DA AKA DAUKE KU ZUWA LOKACIN DA AKA SAMU TAKARDU.

GAME DA DAKUNAN KWANA

JAMI’AR BFSU TA BAYAR DA BAMBANCIN DAKUNAN KWANA DA DAMA.

IDAN BA KA ZAMA A CIKIN JAMI’AR, YA KAMATA A SAMU WURIN DA ZA A KWANA, KUMA YA ZAMA DOLE MAI GIDA YA RAKA SHI OFISHIN ‘YAN SANDAN TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA DON SAMUN TAKARDAR SHAIDA WURIN ZAMA.YAYIN DA AKA YI RAJISTA A JAMI’A, MUDDIN DA AKWAI SHAIDU DAGA OFISHIN ‘YAN SANDAN, ZA A FARA GUDANAR DA HARKOKI DON SHIGA CIKIN JAMI’AR DA SAMUN TAKARDAR ZAMAN KASA.

KADADEN KARATU

FANNONIN KARATU DIGIRI KUDIN KARATU KUDIN RAJISTA

Karatu Don Samun Digiri
Sinanci

Digiri Na Farko

Yuan 12150/Fatarar Karatu

Yuan 22150/Shekara

Yuan 400


Digirgir

Yuan 27000/Shekara

Yuan 800

Fannin Karatu Ba Sinanci Ba

Digiri Na Farko

Yuan 26000/Shekara

Yuan 800


Digirgiri

Yuan 27150/Shekara

Yuan 800


Digirgir A Kwalejin Fassara

Yuan 30000/Shekara

Yuan 800


Digiri Na Uku

Yuan 34000/Shekara

Yuan 800

Karatu Ba Don Samu Digiri Ba
Sinanci

Horarwa

Yuan 11150/Fatarar Karatu

Yuan 21150/Shekara

Yuan 400

WELCOME TO OUR BFSU

ONLINE REGISTRATION

it doesn't take a genius to start and also can become the best person

CLICK HERE

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

OFISHIN KULA DA MU’AMALA DA HADIN GWIWA DA KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA KWALEJIN CONFUCIUS

OFISHIN KULA DA DALIBAI ‘YAN KASASHEN WAJE

OFISHIN KULA DA HARKOKIN YAU DA KULLUM

Copyright@BFSU.Support by ITC