彭龙校长会见(修改尺寸后)

A ranar 17 ga watan Febrairu, shugaban jami’ar BFSU Peng Long ya gana da takwaransa na jami’ar Reading ta Birtaniya David Bell da direktan cibiyar nazarin kimiyya da sadarwar kasuwancin Henry Furfesa Liu Kecheng, inda bangarorin biyu suka tattauna hadin gwiwa tsakaninsu.

Shugaban Peng ya yi maraba da Bell da ya sake ziyarar jami’ar BFSU bayan shekara ta 2013, kuma ya yi farin ciki da ganin hadin gwiwar jami’o’in biyu cikin shekaru da dama da suka gabata, kuma yana fatan jami’o’in biyu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Bayan da Bell ya ji bayani game da bunkasuwar BFSU, ya ce, yana sa ran jami’o’i biyu za su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Bangarorin biyu sun tattauna dalla-dalla game da musayar dalibai da horar da masu neman digiri na uku cikin hadin gwiwa, da yin hadin gwiwa tsakanin kwalejin kasuwanci na jami’o’i biyu a tsakaninsu. Shugaban kwalejin nazarin kasuwanci na kasa da kasa Niu Huayong wanda ya halarci taron.

 

Mujaloli

 

Mujaloli da akan buga a kowane lokaci

Nazari da koyar da harsunan waje(Muhimman)
Adabin kasashen waje (Muhimman)
Dandalin duniya (Muhimman)
Koyar da Rashanci a Sin
Koyon Turanci
Koyon Faransanci
Koyon Rashanci
Nazarin al’adun Jamusanci
Sinanci a kasashen duniya
Koyar da Sinanci a kasashen duniya (Sinanci/Turanci)

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
Ofishin kula da kwalejin Confucius
Ofishin kula da harkokin yau da kullum