Game da BFSU

A safiyar ranar 9 ga watan Disamba, an yi taron shekara-shekara na kwalejin Confucius na kasashen waje a jami’ar BFSU, wannan taro ya kasance taro karo na 11, kuma taken taron shi ne:”Manufar ziri daya da hanya daya da bunkasuwar kwalejin Confucius: sabon kalubale da sabon zarafi.”

Mambobin kwamitin kwalejojin Confucius guda 22 dake kasashe 17 na BFSU sun halarci bikin bude taron.

中国法律与文化年度课程A ranar 21 ga watan Satumba, ma’aikatar kula da ilmi da ma’aikatar kula da harkokin kudi da kwamitin kula da gyare-gyare da raya kasa na Sin sun fidda sanarwar jerin sunayen jami’o’in da kyawawan fannonin karatu da kasar Sin za ta kokarta don raya su, ta yadda za a habaka su har sun zama na gaba-gaba dai a duniya. A cikin sanarwar, jami’ar BFSU ta shiga cikinsu, kuma gwamnatin Sin za ta hobbasa don raya fannonin karatun jami’ar.

A cikin jerin sunayen jami’o’in Sin da kasar za ta kokarta don raya su, an hada da kyawawan jami’o’i 42, da jami’o’in wadanda suke da fitattun fannonin karatu 95, BFSU ta kasance daya daga cikinsu.

北京外国语大学区域与全球治理高等研究院成立大会配图A ranar 22 ga watan Oktoba, an yi bikin kafa kwalejin nazarin hanyoyin daidaita manyan duniya da na shiyya-shiyya a BFSU.

Direktan kwamitin nazarin ilmi da kimiyya da al’adu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Liu Binjie, da mataimakin ministan ilmi na kasar Sin Hao Ping, da mataimakin shugaban sashen kula da tuntubawar kasashen waje kuma direktan hukumar kula da kwararrun kasashen waje a kasar Sin Zhang Jianguo da mataimakin ministan al’adun kasar Sin Ding Wei sun halarci bikin.

Mr. Liu Binjie, da Mr. Haoping, da babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta BFSU Mr. Han Zhen, da shugaban BFSU Peng Long sun sanar da kafa kwalejin tare.

Aikin kwalejin shi ne koyarwa, da nazari, da ba da shawara, gami da horar da kwararru. Ban da wannan kuma, wannan kwaleji zai gudanar da ayyuka don cimma burin taimakawa burin kara tuntubawar kasashen waje, da kirkiro da sabbin tunani wajen kimiyya, da horar da kwararru, gami da buga littattafai da ba da rahoto wajen bayar da sakamakon nazari da aka cimma game da nazarin hanyoyin daidaita manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya. Haka kuma, wannan kwaleji zai kafa tsarin nazari da bude ofishin jami’an diplomasiyya, da ofishin karamin jakadan, da tsarin horar da dalibai masu neman digiri na uku, da tsarin horar da kwararru a jami’a, don gudanar da ayyukan yau na kullum wajen nazari lami lafiya.

彭龙校长会见(修改尺寸后)

A ranar 17 ga watan Febrairu, shugaban jami’ar BFSU Peng Long ya gana da takwaransa na jami’ar Reading ta Birtaniya David Bell da direktan cibiyar nazarin kimiyya da sadarwar kasuwancin Henry Furfesa Liu Kecheng, inda bangarorin biyu suka tattauna hadin gwiwa tsakaninsu.

Shugaban Peng ya yi maraba da Bell da ya sake ziyarar jami’ar BFSU bayan shekara ta 2013, kuma ya yi farin ciki da ganin hadin gwiwar jami’o’in biyu cikin shekaru da dama da suka gabata, kuma yana fatan jami’o’in biyu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Bayan da Bell ya ji bayani game da bunkasuwar BFSU, ya ce, yana sa ran jami’o’i biyu za su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu. Bangarorin biyu sun tattauna dalla-dalla game da musayar dalibai da horar da masu neman digiri na uku cikin hadin gwiwa, da yin hadin gwiwa tsakanin kwalejin kasuwanci na jami’o’i biyu a tsakaninsu. Shugaban kwalejin nazarin kasuwanci na kasa da kasa Niu Huayong wanda ya halarci taron.

 

Jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing (BFSU) tana arewacin zobe hanya na uku dake yankin Haidian a birnin Beijing na kasar Sin, akwai sassan jami’ar guda 2 dake gabas kuma yamma da zoben hanyar, kana jami’ar tana karkashin shugabancin ma’aikatar kula da ilimi ta Sin, ta kasance daya daga cikin fitattun jami’o’in da aka kokari raya su daga watan Mayun shekarar 1998, kuma ta zamanto daya daga cikin shahararrun jami’o’i na jere na farko da gwamnatin Sin ke kokarin raya su kafin farkon karnin 21, kazalika jami’a mai daddaden tarihi ta zama jami’ar dake koyar da harsuna mafiya yawa a kasar Sin.

An kafa sashen koyar da harshen Rashanci na jami’ar yaki da maharan Japanawa ta Sin wato tsohon jami’ar BFSU a shekarar 1941, daga bisani kuma ya bunkasa har ya zama kwalejin koyar da harsunan waje na birnin Yan’an, wanda ke karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, ma’aikatar kula da harkokin wajen Sin ta fara kulawa da shi, har i zuwa shekarar 1954,an canja sunansa zuwa kwalejin koyon harsunan wajen Beijing, kuma a shekarar 1959, an hada shi da kwalejin koyar da harshen Rashanci don ya zamanto sabon kwalejin koyon harsunan waje ta Beijing. A shekarar 1980, ma’aikatar kula da tarbiyan Sin ta fara shugabancin kwalejin, yayin da shekarar 1994, an canja sunansa zuwa jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing.Yanzu, ana iya koyon harsunan waje 98 a jami’ar, wadda ke ikon danka digiri na uku a fannonin adabi da harsunan waje, da adabi da harshen Sinanci, da yada labaru, da siyasa, da dokoki, da tafiyar da harkokin kasuwanci da kimiyya, da gine-gine.

A cikin shekaru 74 da suka wuce, yayin da jami’ar BFSU ta bunkasa bisa bukatun bunkasuwar kasar Sin, ta zamanto wani muhimmin sansanin da ke horar da fitattun dalibai sama da dubu 90 ta fuskokin diplomasiyya, fasara, tattalin arziki da cinikayya, yada labaru, dokoki, da hada-hadar kudi da sauransu bisa akidarta. Idan aka dauki misali da ma’aikatar kula da harkokin wajen Sin, an horar da jakadun kasar Sin a kasashen waje sama da 400,akwai kananan jakadu sama da 1000, saboda haka, aka lakabawa sunan jami’ar BFSU da sunan “ Cibiyar jami’an diplomasiyyan Sin”.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
0086-10-88816715
[email protected] https://international.bfsu.edu.cn/en/
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
0086-10-88816549/0671/6424
[email protected] https://osao.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da kwalejin Confucius
0086-10-88816540
[email protected] https://kzxy.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da harkokin yau da kullum