Shugaban BFSU Peng Long ya raka ministan harkokin ilmi Chen Baosheng ziyarar Japan

Daga ranar 23 zuwa ranar 25 ga watan Maris, shugaban BFSU Peng Long ya raka ministan harkokin ilmin Sin Chen Baosheng ziyarar birnin Hiroshima na kasar Japan, don halartar taron mu’amalar al’adu karo na biyu tsakanin kawacen jami’o’in Sin da Japan, inda suka daddale yarjejeniyoyi da jami’ar Hiroshima, da cimma nasarori da dama.
A ranar 24 ga watan Maris, an yi taron mu’amalar al’adu karo na biyu na kawacen jami’o’in Sin da Japan a yankin Qian Tian na jami’ar Hiroshima na kasar Japan. Ministan harkokin ilmi na Sin Chen Baosheng ya halarci taron, gami da yin jawabi, a madadin kawacen jami’o’in, Peng Long ya yi jawabi.Mutane sama da 80 da suka fito daga jami’o’in Sin da Japan kimanin 22 sun halarci taron.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
0086-10-88816715
[email protected] https://international.bfsu.edu.cn/en/
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
0086-10-88816549/0671/6424
[email protected] https://osao.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da kwalejin Confucius
0086-10-88816540
[email protected] https://kzxy.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da harkokin yau da kullum