An samu sabbin fannonin karatu 18 a jami’ar BFSU

Kwanan baya, ma’aikatar kula da harkokin ilmin kasar Sin ta fidda sakamakon bincike da sabbin fannonin karatu da aka bayar a shekarar 2017. Ma’aikatar kula da ilmi ta Sin ta amince da rokon bude fannonin karatu 18 da jami’ar BFSU za ta gabatar, wadanda sun kunshe da harshen Divehi da harshen Tetum da harshen Dari, da harshen Rwanda, da harshen Lesotho da harshen Burundi, da harshen Chewa da harshen Sango da harshen Fiji da harshen Papua New Guinea da harshen Niuē da harshen Bislama da harshen Maori na tsibiran Cook da harshen Lëtzebuerg da tarihin kasa da kasa, da nazarin kula da kudi, da kasuwancin kasa da kasa da wasan kwaikwayo.
Ya zuwa yanzu, yawan fannin karatu don neman digiri na farko da ake koyarwa a jami’armu ya kai 115, inda yawan fannonin karatu na harsunan waje ya kai 97, kuma akwai harsuna 98 da ake koyarwa, da sha’anin fasara da sauran fannonin karatu da ba na harsuna ba guda 17.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
0086-10-88816715
[email protected] https://international.bfsu.edu.cn/en/
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
0086-10-88816549/0671/6424
[email protected] https://osao.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da kwalejin Confucius
0086-10-88816540
[email protected] https://kzxy.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da harkokin yau da kullum