Shugaban BFSU ya yi jawabi a bikin bude taron kwalejin Confucius karo na 12 na duniya

A ranar 12 ga watan Disamba, an bude taron kwalejin Confucius karo na 12 a birnin Xi’an, taken taron shi ne “Karfafa hadin gwiwa, da kirkiro sabbin tunani da samun bunkasuwa, don ba da gudummawa wajen kafa gamayyar dan Adam.” Mataimakiyar firaministan kasar Sin kuma shugabar cibiyar kwamintin kwalejin Confucius ta Sin Madam Liu Yandong ta halarci bikin bude taro tare da yin jawabi. Shugaban BFSU Peng Long da mataimakinsa Yan Guohua sun halarci taron.

A yayin bikin, a madadin kwalejojin Confucius 220, Peng Long ya yi jawabi, inda ya yi nuni da cewa, a lokacin dunkulewar kasashen duniya baki daya, da zamanintar da harkokin sadarwa, kwalejin Confucius ya taka muhimmiyar rawa wajen kara yin cundaya tsakanin jama’a.

Kwalejin Sofia na kasar Balgariya da BFSU ta dauki nauyin koyarwa, da shugaban kwalejin Munich na kasar Jamus Yakubu Parratt da shugaban jami’ar koyon harsunan waje ta Koriya ta Kudu Kim Renzhesun samu lambobin yabo “Kyakkyawan kwalejin Confucius” da “Fitaccen mai ba da taimako.” Yayin da kwalejin Confucius ta Malaysia ta samu lambar yabo wadda ta yi fice wajen shirya jarrabawar Sinanci.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
0086-10-88816715
[email protected] https://international.bfsu.edu.cn/en/
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
0086-10-88816549/0671/6424
[email protected] https://osao.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da kwalejin Confucius
0086-10-88816540
[email protected] https://kzxy.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da harkokin yau da kullum