An kafa kwalejin Beiwai da kwalejin nazarin kungiyar kasa da kasa a BFSU

配图A ranar 9 ga watan Afrilu, an yi bikin bude kwalejin Beiwai da kwalejin nazarin kungiyar kasa da kasa a jami’ar BFSU, direktan sashen kula da harkokin jami’i na kwamintin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Sun Xueyu da direktan sashen kula da jami’o’i na ma’aikatar ilmin Sin Zhang Daliang da babban sakataren jami’ar Han Zhen da shugaban jami’ar Peng Long sun halarci bikin bude kwalejin.

Sabbin kwalejojin da aka bude a wannan karo zai kokarta hadin gwiwa tsakanin mabambanta kwalejoji da sassa na jami’ar, don yin gyare-gyare game da tsarin horar da dalibai, wadanda ke kokarin neman digiri na farko a jami’ar, ta hakan za a yalwata ilmin dalibai, da horar da ikon nazarinsu, da horar da fitattun daliban da ke da halayyen musamman na BFSU. Manyan ayyukan kwalejin Beiwai su ne, sabunta tsarin horar da dalibai masu neman digiri na farko, da lalubo tsarin horar da dalibai masu iya harsuna da dama,kuma wadanda ke da ilmi daga duk fannoni, ta hakan za a horar da fitattun dalibai ga kwalejin nazarin kungiyar kasa da kasa.

A matsayin wani aikin gwaji da jami’ar BFSU ta yi wajen horar da dalibai da raya jami’ar, za a yi amfani da tsarin shirya jarrabawa da kansa, da kafa sabon tsari game da makin karatu, da tsarin zaben darussa, da dai sauransu. Bayan da aka inganta wannan tsari, za a yi amfani da tsarin a cikin duk jami’ar, don karfafa ingancin dalibai na BFSU.

Dalilin da ya sa aka kafa kwalejin nazarin kungiyar kasa da kasa a jami’ar BFSU shi ne don nazarin tsarin horar da dalibai masu ilmi daga duk fannoni da kungiyar kasa da kasa ke bukata, kuma wannan shi ne gyare-gyare da jami’ar ta yi wajen karfafa tsarin koyarwa. Kwalejin nazarin kungiyar kasa da kasa zai yi kokari don horar da dalibai da nazarin hukumomi da kafa wani dandali ga dalibai don su shiga kungiyoyin kasa da kasa. Ban da wannan kuma, wannan kwaleji zai zama wani sansanin kafa fannonin karatu daban daban na jami’ar, kuma zai zama wani sansanin nazarin kungiyar kasa da kasa, kana zai zama wani sansanin horar da dalibai da fitar da su zuwa kungiyar kasa da kasa. Wannan kwaleji yana da halayye musamman guda 3, na farko shi ne za a kafa tsarin malami horar da dalibi kai tsaye a kwalejin, sannan kuma za a kafa sabon tsarin darussa da hanyar horar da dalibai a kwalejin, na karshe shi ne za a kafa sabon tsarin tafiyar da harkoki a kwalejin.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
0086-10-88816715
[email protected] https://international.bfsu.edu.cn/en/
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
0086-10-88816549/0671/6424
[email protected] https://osao.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da kwalejin Confucius
0086-10-88816540
[email protected] https://kzxy.bfsu.edu.cn/
Ofishin kula da harkokin yau da kullum