An yi bikin kafa kwalejin nazarin wayewar kai ta duniya da mu’amala al’adu a BFSU

%e5%8c%97%e4%ba%ac%e5%a4%96%e5%9b%bd%e8%af%ad%e5%a4%a7%e5%ad%a6%e6%af%94%e8%be%83%e6%96%87%e6%98%8e%e4%b8%8e%e4%ba%ba%e6%96%87%e4%ba%a4%e6%b5%81%e9%ab%98%e7%ad%89%e7%a0%94%e7%a9%b6%e9%99%a2%e6%88%90

A ranar 6 ga watan Disamba, an yi bikin kafa kwalejin nazarin wayewar kai ta duniya da mu’amalar al’adu a jami’ar BFSU. Shugaban hadadden kwamintin nazarin ilmin Confucian Teng Wensheng da direktan cibiyar kula da zamantakewar al’umma da kimiyya ta ma’aikatar ilmin Sin Zhang Donggang, da babban sakataren jami’ar BFSU Han Zhen da shugaban jami’ar Peng Long sun halarci bikin.

Makasudin kafa kwalejin shi ne, a kokarta don raya nazarin al’adu da tarihi, da addini, da filsafa, da fasaha a jami’ar, don kara ba da gudummawa wajen kyautata jami’ar. Za a bi ka’idar yin koyi ga wayewar kai tsakanin kasashen duniya, da yin amfani da fiffikon harsuna da dama da ake koyarwa a jami’ar BFSU, don raya ilmin nazarin wayewar kai ta gida da waje, da tarihi, da addini, da filsafa a duniya, ta hakan za a nuna ma’anar musamman ta wayewar kai a Sin da duk duniya baki daya.

Tsohon shugaban jami’ar Northwest Zhang Qizhi zai zama shugaba mai daraja na kwalejin, babban sakataren Han Zhen zai zama direktan kwamintin nazari na kwalejin, yayin da shugaban BFSU Peng Long zai zama direkta mai ba da umurni, kuma Furfesa Zhang Xiping zai zama shugaban dake kula da ayyukan yau da kullum na kwalejin.

NO.2 North Xisanhuan Road Haidian District Beijing

Ofishin kula da mu’amala da hadin gwiwa da kasashen waje
Ofishin kula da dalibai ‘yan kasashen waje
Ofishin kula da kwalejin Confucius
Ofishin kula da harkokin yau da kullum